Kotu ta soma sauraren karar Jama'i'yar CPC kan zaben shugaban kasa a Najeriya

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa a Najeriya ta fara sauraron karar da jam'iyar CPC ta shigar tana kalubalantar nasarar shugaba Goodluck Jonthan ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan jiya.

Jam'iyar CPC ta bukaci kotun ta tilasta wa hukumar zabe ta ba ta damar samun wasu muhimmman takadun da aka yi amfani da su a zaben.

Tace za ta yi amfani da takardun ne wajen kalubalantar nasarar da hukumar zaben ta ce shugaba Goodluck ya samu.