Gwamnatin Nijar za ta binciki ayyukan hako ma'adinai a kasar

Wata masana'antar sarrafa karfen Uranium
Image caption Nijar tana da arzikin karfen Uranium

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta ce za ta binciki ayyukan kamfanonin hakar ma'adinai a kasar don tabbatar cewa baa zaluntar kasar.

Firayim ministan Nijar din ne, Malam Brigi Rafini ya bayyana hakan a lokacin wani taron maneman labarai da ya kira yau a birnin Yamai.

Hakazalika, Malam Birgi Rafini ya yi karin haske kan korafe korafen da wasu yan kasar ke yi a kan wasu matakai da gwamnatin Nijar din ta dauka, tun bayan hawanta kan karagar mulki.

Korafe-korafen dai sun shafi batun nada wasu sojoji a kan mukamin gwamnan jihar Agadez da na jihar Diffa da kiran da wasu kungiyoyin kare Demokradiyya suka yi na a binciki gwamnati mulkin sojan da ta gabata da kuma matsalar dauke wutar lantarki da ake fama da ita a kasar.