Sarauniya Elizabeth na ziyara a Ireland

Image caption Sarauniya Elizabeth

Sauraniya Elizabeth na ziyarar yini hudu zuwa Ireland. Wanan shi ne karon farko da sarauniyar za ta ziyarci jamhuriyar tun bayan lokacin da ta samu 'yanci.

Wanan shine karon farko da shugabar kasar Burtaniyar zata kai ziyara tun bayan lokacin da jamhuriyar Ireland din ta samu yancin kai daga Birtaniyar shekaru 90 da suka wuce.

Rundunar yansanda ireland da ake kira Gada na shirin girka abun da ta kira matakin tsaro mafi girma a tarihin kasar.

Sarauniyar dai zata kai ziyara zuwa wasu wurare da ake cece kuce akan tahirinsu, da suka hada da filin wasani na crok park, inda a nan ne aka gudanar da mummunan kisan nan da ake kira bloody sunday a shekerar 1920 da kuma lambu tunawa da magabata a birnin Dublin.

Manufar ziyarar dai ita ce a nuna cewa kasashen biyu sun samu cigaba daga matsalolin da suka rika fuskanta a baya.

Sai dai kuma ana ganin ziyarar zata tunzura ra'ayoyin wasu da suka yi amana gwamnatin Ireland be kamata ta yi marhaban lale ga sarauniyar Birtaniyar ba yayinda kawo yanzu kawunan jama'ar ireland din a rarabe yake.