Kotun Burtaniya ta Umarci a biya wasu 'yan Najeriya diyya

Image caption An bautar da matan uku ne a Burtaniya

Wata babbar kotu a Burtaniya ta umarci a biya wasu 'yan mata yan asalin Najeriya su hudu diyyar fam dubu ashirin, bayan da aka shigar dasu kasar ba bisa ka'ida ba.

Alkalin kotun ya ce bincike ya nuna cewa 'yansandan Burtaniya sun take hakkin matan, ta hanyar kasa gudanar da binciken kan korafin da suka gabatar.

An dai bautar da matan ne bayan da aka shiga da su kasar. Hukumar yansandan Burtaniya ta bayyana rashin jin dadi kan yadda lamarin ya afku.

Alkalin kotun Mr Justice Wyn Williams, ya umarci a biya kowace daya daga cikin matan fan dubu biyar, kwatankwacin naira miliyan daya da dubu 250, bayan da ya yanke hukuncin cewa yan sandan Burtaniya sun gaza wajen gudanar da cikakken bincike - wanda hakkan ya sabawa dokokin kare hakkin bil'adama na tarayyar Turai.

Matan wadanda ba a bayyanasu ba, saboda dalilai na shari'a, sun zargin an kaisu Burtaniya ne daga Najeriya ba bisa ka'ida ba, sannnan aka sanyasu yin aiki a wasu gidaje a birnin Landan na tsawon shekaru ba tare da ana biyansu ba, sannan iyayen gidannasu suka ci zarafinsu ta hanyoyi da dama.

Sun yi korafin cewa 'yansandan Burtaniya sun tauye musu hakki karkashin dokar kare hakkin bil'adama ta Turai, ta hanyar kasa gudanar da bincike a lokaci mai tsawo.

A Lokacin shari'ar dai yansandan sun musanta zargin.

Matan sun ce anci zarafinsu ta hanyar sanya su yin wasu ayyuka da suka saba hankalin bil'adama wadanda suka hada harda bauta.

BBC ta tuntubi maimagana da yawun Hukumar hana fataucin mutane ta kasa Najeriya, Arukwe Arinze, ta waya domni jin martanin da za su mayar kan hukuncin sai ya ce:

"Munyi farin ciki domni kamata yi wadanda suka jefa rayuwar wasu cikin wahala da cin zarafi su ma a sasu su ji a jikinsu.

"Don haka wannan batu na daga cikin gyran da muke so a yiqwa dokar da ta kaaf wannan hukuma, ta yadda duk wanda ya ci zarafin wani to mashi ba zai sha ba.

Ana ta bangaren hukumar 'yansandan Burtaniya, ta fitar da sanarwa inda ta nuna damuwa kan lamarin, sannan ta ce akwai matakai da dama data dauka domin ganin an kawo karshen irin wadannan halaye na cin zarafin masu karamin karfi kasar.