Tankiya kan karba karba a majalisun kasa

Taron jam'iyyar PDP Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gangamin taron jam'iyyar PDP

Kundin tsarin mulkin Jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya, ya ayyana cewar domin samar da tafarkin daidaito da adalci da kuma gaskiya, jam'iyyar za ta kiyaye da manufar kewayawa da mukamai, na siyasa da na gwamnati tsakanin shiyoyin Nigeriya.

An bullo da wannan tsari ne domin tabbatar da ana damawa da kowane bangare a harkokin mulkin kasar.

To sai dai a zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP gabanin zaben shugaban kasa, jam'iyyar PDPn ta yi watsi da wannan tsari na karba karba,a lokacin zaben shugaban kasa.

To amma a yanzu da aka kammala zabubbukan, yayin da ake tunkarar wadanda za su jagoranci majalisun dokokin kasar, jam'iyyar ta PDP ta ce tilas ne ayi amfani da tsarin na karba-karba wajen zabar wadannan shugabannin. Wannan batu dai na ci gaba da haifar da cece-kuce a majalisar dama kasar baki daya.

To shin Jam'iyyar PDPn ta yi amai ta lashe ne a kan wannan magana, ko kuwa yaya al'amarin ya ke? Domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato baki da dama da suka hada da, Ambasada Ibrahim Kazaure, Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP na kasa shiyyar arewa maso yamma, da Hon. Musa Sarkin Adar, Shugaban kwamitin kula da harkar zabe na Majalisar wakilai ta Najeriya da Alhaji Bashir Jantile wani dan siyasa a Najeriya da Malam Kabiru Sufi, Malami a kwalejin Fasaha da Kimiya ta Kano.