Kotu ta ce a biya Farfesa Okereke-Onyiuke diyya

Hedkwatar kasuwar saida hannayen jari ta Najeriya
Image caption Hedkwatar kasuwar saida hannayen jari ta Najeriya

A Najeriya, yau ne babbar kotun tarayya da ke birnin Legas ta yanke hukuncin cewa hukumar da ke sanya ido a kasuwar saida hannayen jarin kasar, ta yi kuskure wajen korar tsohuwar shugabar kasuwar, Farfesa Ndi Okerere-Onyiuke.

Kotun ta bai wa hukumar umarnin biyan Farfesa Okerere-Onyiuke Naira miliyan 500, sakamakon gangancin da ta ce hukumar ta yi wajen korar tsohuwar shugabar kasuwar.

Sai dai hukumar ta ce zata daukaka kara kan batun.

A bara ne dai hukumar dake sanya ido a kasuwar sayar da hannayen jarin ta cire Farfesa Okerere-Onyiuke daga shugabancin kasuwar, bayan da ta zarge ta da kashe kudaden kasuwar ta hanyoyin da ba su dace ba.

Lamarin da ya kai Farfesa Okerere-Onyiuken kalubalantar matakin a gaban kotu.