Ziyarar Ban Ki Moon Najeriya

Ranar Lahadi 22 ga watan Mayu ne ake sa ran Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon zai fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Najeriya.

Babban Sakataren zai tattauna da Shugaban Kasar Najeriya kan batutuwan da suka hada da cimma muradun karni na Majalisar dinkin duniyan wato MDGs.

Haka zalika zai kuma gana da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki a Kasar, tare kuma da kai ziyara wasu kananan asibitoci a babban birnin tarayya Abuja.

Tun a baya ne dai aka saka ran zuwan Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar, amma bai samu damar zuwa ba sai wannan karon.