Kwana na biyu a Ziyarar Ban Ki Moon Najeriya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya ce Majalisar Dinkin Duniya ta dukufa wajen yaki da mutuwar mata da yara 'yan kasa da shekaru biyar da haihuwa.

Ban Ki Moon ya yi wannan jawabin ne a yayin da ya ke wata ziyarar aiki a Najeriya domin duba in da aka kwana akan batun cimma Muradun Karni na Majalisar Dinkin Duniya wato MDGs.

A yau ne dai aka shiga rana ta biyu ta ziyarar da Sakatare Janar din ke yi a Kasar.

Batun rage talauci a tsakanin al'umma ma na daga cikin kudirin Muradun Karni na Majalisar Dinkin Duniya, wanda Najeriya ke son cimma nan da shekarar 2015.

To sai dai duk da ikirarin da Hukumomin Kasar ke yi na cewa suna daukar matakan rage talauci, masana tattalin arziki a yankin kudu maso gabashin Kasar na ci gaba da tsokaci kan yadda talauci yayi kamari a tsakanin jama'a, musamman al'ummomin dake yankin Arewacin Kasar.

Bincike dai ya nuna cewa, a cikin shekaru fiye da ashirin da suka gabata, tattalin arzikin jama'ar Kudancin Najeriya na ci gaba da bunkasa, yayin da a bangare daya kuma na takwarorinsu dake Arewaci ke fama da koma baya.

Baya ga batun cimma muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya, ana tunanin Babban Sakataren zai gana da Shugaban Kasa idan an jima.