Zargi: Majalisar Dokokin Najeriya ta kara Kasafin kudi

Hakkin mallakar hoto AP

Da alama tsugunne ba ta kare ba dangane da batun kasafin kudin Najeriya na bana.

Wasu rahotanni na zargin cewa, 'yan Majalisar Wakilan Kasar sun kara kudi har Naira Biliyan Dari Biyu a cikin kasafin kudin da suka gabatarwa Shugaban Kasa.

To sai dai 'yan Majalisun sun musanta wannan zargi in da suka bayyana cewa zance ne wanda bashi da tushe balle makama.

Tun farko dai Majalisar Dokokin Najeriya ta yi kari ne akan kasafin kudin da Shugaban Kasa ya mika mata a watan Disambar bara.

Kamar dai yadda dokar kasar ta tanadar, duba kasafin kudi da bangaren zartarwa ya mikawa Majalisar na daga cikin muhimman ayyukan 'yan Majalisun Dokoki.

A bangare guda kuma, yayin da ya rage 'yan kwanaki Majalisar Dokoki ta tarayya ta bakunci sabbin 'Yan Majalisu, wasu na ganin 'yan Majalisar Dokoki masu barin gado basu taka rawar a zo a gani ba, musamman ta fuskar kafa dokokin da za su amfani talakawa da mazauna yankunan karkara.

Sannan ana ganin basu yi wani abin a zo a gani ba wajen sa ido akan aikace- aikacen bangaren zartarwa.

Sai dai 'Yan Majalisar sun musanta wannan zargi.