Tsarin kiwon Lafiya a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP

A kasashe masu tasowa matsalolin kula da lafiya na daga cikin abubuwan dake tauye cigaban al'umma da hukumomi kan su.

Haka ne ma ya sa Majalisar Dinkin Duniya tare da gwamnatocin irin wadannan kasashen ke kokarin samun mafita.

Daga ciki sun hada da samarda kananan asibitoci a yankunan karkara domin kula da lafiyar mata da kananan yara bisa shirin nan na muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya wato MDGs.

Sai dai kuma a wasu asibitocin sau tari akan bar al'umma ne da daukar nauyin kansu, duk kuwa da cewa ya kamata a ce sun sami wasu abubuwan kyauta.

Wannan lamari ne ma ya sa wasu masu lura da al'amura ke ganin cewa bai kamata a bar kula da wadannan asibitocin a hannun al'umma ba.