Badakala a Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya

A Najeriya bisa ga dukkan alamu dai za'a kai ruwa rana tsakanin Jam'iyyar PDP da mambobinta dake Majalisar wakilan Najeriya saboda dagewar da wasu 'yan Majalisar suka yi akan cewa, ba zasu bi tsarin jam'iyyar ba wajen fidda wanda zai zama kakakin Majalisar.

Ita dai jam'iyyar PDP tuni ta mika mukamin kakakin Majalisa ga yankin kudu maso yamma.

Sai dai wasu daga cikin 'yan Majaliasar na cewa, akan wannan batu ba zasu yi biyayya ga jam'iyyar tasu ba.

Sun dai bayyana cewa muddin aka hana su zabar wanda suke so, to kamar an yi fatali ne da tsarin demokradiyya.