Shugaban Nijar ya kaddamar da aikin dam

Hakkin mallakar hoto bbc

A Jamhuriyar Nijar, a yau ne Shugaban Kasar Alhaji Mahammadou Issoufou ya jagoranci bikin kaddamar da aikin gina madatsar ruwa ta Kandaji a kogin kwara da aka fi sani da kogin Isa dake Jihar Tillbery, a yammacin kasar.

An kiyasta cewa madatsar ruwan zata baiwa Kasar Nijar din akalla filin Noma na zamani sama da ekoki dubu daya da dari bakwai.

Bugu da kari, madatsar ruwan zata samar wa Kasar hanyar samun makamashi kimanin Megawatt dari da talatin da biyu.

To sai dai aikin madatsar ruwan ka iya haddasa kaurar dubban mutane daga gidajen su.