Kanar Abdoulaye Bague ya yabawa kotu a Nijer

Hakkin mallakar hoto bbc

A jamhuriyar Nijar a karo na farko tun bayan da kotu ta wankesu daga zargin juyin mulkin da aka tuhume su da shi, tsohon sakataren majalisar koli ta tsohuwar gwamnatin mulkin sojan kasar CSRD, Kanal Abdoulaye Bague ya yi magana a yau inda ya nuna jin dadinsa da yadda kotu ta yi musu adalci.

Dangane da maganar ko zai dau kakinsa na soja, kanal din ya ce babu abin da zai hana shi ganin cewa zargin da aka yi ma shi bai tabbata ba.

Sai dai bai bayar da haske ba a kan maganar ko zai shigar da kara domin neman diyya bisa kagen da aka yi ma shi.