Ana gwagwagwa tsakanin gwamnatin Filato da manyan likitoci

Rahotanni daga jihar Filato dake tsakiyar Najeriya, na cewa ana ci gaba da gwagwagwa tsakanin gwamnatin jihar da kuma mayan likitoci wadanda suka dauki lokaci mai tsawo suna yajin aiki.

Suna gudanar da yajin aikin ne dangane da sabon tsarin albashi da gwamnatin tarayyar kasar ta bullo da shi ga likitoci. Manyan likitocin dai da ake kira Resident Doctors na neman gwamnatin jihar ta aiwatar da sabon tsarin albashin ne da ake kira CONMESS, amma gwamnatin jihar ta ce ba ta da isassun kudaden da za ta biya sabon tsarin albashin, abun da ya sa likitocin suka sha alwashin cigaba da yajin aikin.

A bangare guda kuma marasa lafiya dake fama da munanan cututtuka a fadin jihar na cigaba da shan wahala wajen samun magani.