Zan bada iznin kai hari kan Alqaeda da Taliban a Pakistan-Obama

Shugaba Obama ya ce a shirye ya ke ya bada umarnin kai wani sabon farmaki a kan shugabannin al Qaeda da Taliban a Pakistan, duk da cewa kisan Osama bin Laden a kasar ya janyo tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu.

A wata hira ta musamman da BBC, Mr Obama ya ce Amruka tana mutunta 'yancin Pakistan, amma ba za ta iya kyale wasu mutane a kasar su shirya makarkashiyar kai hare-hare a kan Amruka da kawayenta, ba tare da daukan mataki a kan su ba.

Wakilin BBC a Pakistan ya ce kalaman na Mr Obama ba za su faranta ran hukumomin kasar ba, wadanda suka ji kunya matuka, ba kawai ganin cewa an gano Osama bin Laden a kasar ba, a'a har ma da yadda Amruka ta yi gaban kanta wajen daukan matakin da ya kai ga hallaka shi.