'Kasashen Afrika da ke yankin kudu da sahara na baya'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bayyana cewa kasashen Afirka da ke yankin kudu da hamadar sahara sun kasance kurar-baya a kokarin da ake yi na cim ma muradan karni.

Ya ce matukar ba su kara kaimi ba to da wuya su kai labari nan da shekaru hudu masu zuwa.

Mr Ban Ki Moon wanda ke ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Najeriya ya jaddada cewa cim ma muradan, musamman inganta lafiyar iyaye mata da kananan yara zai taimaka wajen kyautata rayuwar al`umomin duniya baki daya.

Mr banki Moon wanda ya yi wa manema labaru bayani bayan ganawarsa da shugaban Najeriya da wasu jami`an gwamnati ya ce kasashe da dama a bangarorin duniya suna bakin kokarinsu wajen ganin sun cimma muradan karni nan da shekaru hudu masu zuwa.

Cimma maradun karni

Amma ya yi tsokacin cewa kasashen Afirka da da ke yankin kudancin hamadar sahara na da sauran aiki a gabansu.

"Wasu daga cikin muradan karni na makarewa, musamman a kasashen Afirka da ke yankin kudu da hamadar sahara.

"Kasashe da dama sun yi abin kirki daidai gwargwado wajen cimma muradan karni da suka shafi yaki da talauci da samar da ilimi da kuma rage mace-mace da cututtuka irin su zazzabin cizon sauro, da Sida ke haddasawa.

" Wani burin da kasashe ke tafiyar hawainiya wajen cimma masa shi ne batun shawo kan mace-mace iyaye mata da kananan yara sakamakon cututtukan da za a iya yin riga-kafinsu." In ji Ban Ki Moon

Sakataren dai ya yaba da tsarin da Najeriya ke bi wajen wajen shawo kan wannan matsalar, amma ya jaddada bukatar da ke akwai ta matsa-kaimi wajen cimma wannan burin nan da shekaru hudu masu zuwa.

Su ma kungiyoyin farar-hula da ke sa-ido a kan ayyukan kasashen duniya don cimma maradan karnin na da ra`ayin cewa da wuya kasashe irin Najeriya su kai ga nasara ba tare da sun sake lale ba.

Gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi na daga cikin wadanda ake zargin ce ba sa ba da kason da ya dace wajen cimma wannan buri.

A shekara ta dubu biyu da sha biyar ne dai majalisar dinkin duniyar ke sa-ran cimma ma mradan nata guda takwas, wadanda ta ce za su taimaka wajen inganta rayuwar al`umomin duniya baki daya.