Kungiyoyin Kaduna na taimakawa 'yan gudun hijira

A Jihar Kaduna dake arewacin Nigeria, wasu kungiyoyi masu zaman kansu na kokarin taimakawa mutanen da suka yi kaura daga muhallinsu, sakamakon rikicin siyasar da ya barke a lokacin babban zaben da aka yi a kasar a watan da ya wuce.

Baya ga samawa 'yan gudun hijirar kayayyakin masarufi, kungiyoyin suna kuma kokarin ilimantar da su, musamman kananan yara, 'yan firamare da sakandari, kafin su samu damar komawa garuruwan su.

Irin wannan makaranta da kungiyoyin suka samar na karantar da yara kanana ne 'yan Firamare da kuma matan aure, wadanda ake sa ran za su ci gaba da karatun su da zarar sun koma garuruwan su.

Kungiyoyin dai na ci gaba da karantar da yaran a sansanonin 'yan gudun hijira wadanda suka baro gidajen su a sanadiyyar rikicin siyasar da ya rikide zuwa na addini da kabilanci.

Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin da aka yi fama da rikicin bayan zaben Shugaban Kasa da aka yi a watan Afrilun da ya gabata.