Zargi: PDP na shirya makarkashiya a Majalisa

Hakkin mallakar hoto AP

A Najeriya, yayin da ake sa-ran Majalisar Wakilan Kasar za ta ci gaba da zamanta a yau din nan, wasu `ya`yan Majalisar na zargin cewa jam`iyyar PDP mai mulkin kasar na kitsa makircin yadda za'a warware shawarar da Majalisar ta yanke na amfani da kada kuri`a cikin sirri idan suka zo zaben Shugabannin Majalisar.

A makon jiya ne dai Majalisar ta amince da tsarin kada kuri`a cikin sirri, tsarin da wasu Mambobi suka ce zai taimaka wajen zaba musu Shugabanni ba tare da ya bar baya da kura ba.

Sai dai kuma wasu 'yan Majalisar karkashin inuwar Jamiyyun adawa sun ce sam ba za ta yiwu ba.

Suma dai wasu daga cikin Mambobin Majalisar karkashin inuwar Jam'iyyar PDP mai mulki, sun ce hakan ka iya haddasa kiyayya a tsakanin Mambobin Majalisar.