Masu AIDS sun yi zanga zanga a Gusau

Wasu kungiyoyin masu fama da cutar AIDS ko SIDA, da kuma na masu fafutukar kare hakkinsu, sun gudanar da zanga-zangar lumana a Gusau, domin kokawa da jinkirin da suka ce majalisar dokokin jihar Zamfara ta yi, wajen amincewa da dokar kafa hukumar yaki da cutar kanjamau a jahar.

Rahotanni sun nuna cewar, kudurin neman kafa hukumar ya kwashe fiye da shekara daya a gaban majalisar.

Majalisar dokokin dai ta ce ta karbi koken mutanen kuma zata yi nazari a kansa.