Za a tuhumi shugaba Mubarak da kisan kai

Tsohon shugaban Masar, Mubarak Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tsohon shugaban Masar, Mubarak

Jami'ai a kasar Masar sun ce za a tuhumi tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak , da 'ya'yansa da laifin kisan kai na masu zanga zanga, a lokacin tarzomar da ta yi sanadiyar kawar da shi daga mulki cikin an Fabrairu.

Haka nan kuma za a tuhume su dalaifin cin hanci da rashawa.

Kungiyoyin kare hakkin jama'a sun ce an kashe daruruwan jama'a, a lokacin zanga zangar.

Ana tsare da Mubarak mai shekaru 83 ne ,a wani asibiti, a garin yawon shakatawa na Sharm el-Sheikh .

'Ya'yan nasa biyu kuma, Gamal da Alaa , ana tsare da su ne a wani gidan kaso dake birnin Alkahira.