Shugaba Jonathan ya mayarwa Majalisa kasafin kudi

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya bisa dukkan alamu tsugune bata kare ba akan batun kasafin kudin Kasar na bana.

Shugaba Goodluck Jonathan ya mayarwa Majalisun Dokokin Kasar kasafin kudin inda ya bukaci 'yan Majalisun da su sake yin nazari akansa.

Shugaba Jonathan ya aike da wasiku daban- daban ga Majalisun Dattijai da na Wakilai in da ya bukaci su sake yin garanbawul a kasafin kudin.

Matakin Shugaban dai ba zai rasa nasaba da zargin kara yawan kudaden da gwamnati zata kashe a bana ba, inda ake zargin 'yan Majalisar sun yi kafin su amince da kasafin kudin a makon daya gabata.