Ana ci gaba da artabu a Yemen

Ana ci gaba da artabu kan titunan Sanaa, babban birnin Yemen a rana ta uku, tsakanin dakarun tsaro, da na kungiyar kabilar kasar mafi karfi , wadda ta shiga cikin boren da ake yi kan Shugaba Ali Abdullah Saleh.

Ya zuwa mutane arba'in ne suka mutu a fadan da ya barke jiya, Litinin, bayan dakarun tsaro sun kai samame a gidan shugaban kabilar, Sheikh Sadiq Al-Ahmar.

Rahotanin sun ce bisa dukkan alamu an yi wa gidan ruwan harsasai, yayinda shugabannin kabilar ke kokarin shiga tsakani, domin ganin an tsagaita wuta.

Shugaba Saleh ya zargi Sheikh Al Ahmar da kokarin haddasa yakin basasa.