Shugaba Goodluck ya fasa halartar taron G8

Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya soke ziyarar da zai kai taron koli na G8 da ake yi a kasar Faransa.

A wata sanarwa da mai baiwa shugaban shawara a harkar yada labarai ya sanyawa hannu, Mista Ima Niboro, ta ce soke ziyarar ta biyo bayan tokar aman dutse a kasar Iceland wanda kuma ke kawo cikas ga harkokin zirga-zirga a Turai.

Mahukunta a harkar sufuri sun nuna fargabar cewa za'a iya samun tokar aman dutsen, wanda kuma zai iya kawo cikas ga dawowar Shugaba Jonathan kan lokaci domin a rantsar da shi a kan kujerar shugabanci a ranar Lahadi, bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Afrilu.

An dai sa ran cewa Shugaban kasar zai halarci taron koli na G-8 ne a Deauville da ke Faransa a ranar juma'a, sannan kuma ya dawo ranar Asabar, kafin a rantsar da shi a ranar Lahadi.