Huldar Kanal Gaddafi da kungiyoyin yakin sunkuru a Latin Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kanal Gaddafi

Huldar siyasa da horon amfani da makamai tsakanin Kanal Gaddafi da kungiyoyin sunkuru a Latin Amurka ya kai tsawon shekaru arba'in da suka wuce.

"A shekarun 1980 ne, kungiyoyin sunkuru da kuma gwamnatin Libya suka fara zumunci." In ji León Valencia, wani tsohon kwamandan kungiyar National Liberation Army a Columbia.

"Amma kafin lokacin, bangarorin biyu na da akida guda ne."

Valencia ya shiga rayuwar farin kaya ne a shekarar 1994, kuma a yanzu haka shi ne Shugaban kamfanin New Rainbow Corporation, wanda ke shirin hadin kan 'yan siyasa a Columbia, kuma me fada aji a harkar siyasa.

Valencia ya ce, kungiyoyin sunkuru a Columbia sun karu sosai da akidojin kanal Gaddafi, musamman ma kundin tsarin mulkin Gaddafi da ake kira "Green Book".

Akidoji

"Akidar da Gaddafi ya bullo da ita ta sha babban dana tarayyar Soviet wadda kuma mutanen Columbia ke adawa da ita." In ji Valencia.

Saboda akidar Gaddafi da kungiyoyin sunkuru a Latin Amurka, Kanal Gaddafi ya taimaka wajen bunkasar su.

Image caption Shugabannin kasashen latin Amurka

Wani rahoto da hukumar leken asirin Amurka ta CIA ta rubuta a shekarar 1986, ya yi nuni da cewa kasar Libya na bada agajin makamai da kuma kudi a kungiyoyin sunkuru a kasashen Colombia da Chile da Ecuador da kuma kila Peru.

A wannan lokacin Libya na huldar diplomasiya da kasashen Cuba da kuma Nicaragua.

BBC tayi kokarin jin ta bakin jami'an Libya da ke ofishin jakadanci a Caracas, game da huldar dake tsakanin gwamnatin Libya da kungiyoyin sunkuru a kasashen latin Amurka amma jami'an diplomasiyya a ofishin sun ce ba za su iya cewa komai ba akan al'amarin.

Dabaru rarrabuwan kawuna

A shekarar 1982, lokacin da ake dimuwar yakin nukiliya a kasashen Turai da Amurka, CIA ta nuna damuwa, kan kokarin tarrayar Soviet wajen amfani da Kanal Gaddafi, domin karfafa kungiyoyin sunkuru a kasashen Latin Amurka.

"Tarrayar Soviet na kara wa Libya kwarin gwiwa domin baiwa kungiyoyin sunkuru kudade da makamai da nufin kafa akidar Soviet a yankin Latin Amurka da kuma Caribbean." In ji wani rahoton CIA.

Amma in ji Erik Flakoll Alegria, Gaddafi na tare da Frente Sandinista, tun kafin nasarar kungiyar 'yan tawayen ta Nicaragua a watan Yulin shekarar 1979.

"Tomás Borge shugaban 'yan tawaye a Nicaragua a wannan lokacin ya garzaya Libya bayan nasarar da ya samu fiye da sau guda kuma tare da ni aka yi tafiyar." In ji Flakoll.

"Mun samu taimako daga Libya matuka. Kuma mun samu miliyoyin daloli." In ji Flakoll a hirarsa da BBC.

"An turo mana da makamai ta jiragen ruwa daga Libya zuwa Nicaragua da kuma El Salvador."

"Gaddafi dai bai bukaci wani abu ba. Yana so ne kawai a rika kaiwa kungiyoyi dake da alaka da Amurka, ya bukace su da su rika kaiwa ofisoshin jakadu hari." In ji Valencia.

Har wa yau, wani shugaban kungiyar sunkuru ya ce, kungiyoyin ba su yi abun da Gaddafin ya bukace su da su yi ba.

A watan Fabrairun wannan shekarar -kwanaki kadan kafin a fara rikicin siyasa a Libya, Babban bankin Nicaragua ya bayyana yarjejeniya da Libya na soke bashin da Libya ke binta wanda ya kai dalar Amurka miliyan 195.8 cikin dala miliyan 313.6 wanda ta karba tun a shekaru alif dari tara da tamanin.

Wasu dai na ganin yafe bashin da Libyan tayi yayi nuni da irin dadaddiyar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.