Yau Masar za ta bude iyakarta da Gaza

Falasdinawa masu jiran bude iyakar Gaza Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Falasdinawa masu jiran bude iyakar Gaza

Masar ta ce yau za ta bude iyakar ta da Zirin Gaza, al'amarin da zai kawo karshen killace yankin da aka yi tun shekarar 2007 lokacin da Hamas ta karbe iko.

Hakan na nufin a karo na farko a cikin shekaru hudu, mutanen Gaza za su samu kwarya-kwaryar damar ketara iyakar yankin zuwa Masar.

Har yanzu dai Falasdinawa maza 'yan shekaru goma sha takwas zuwa arba'in za su bukaci takardar izini, wato visa, kafin su shiga Masar—baya ga su kuwa, cikin sauki kowa zai iya shiga kasar ta Masar.

Sai dai duk da haka, ana sa ran wannan mataki, wanda zai baiwa maziyarta damar shiga da fita, ya kuma farfado da harkokin kasuwanci, zai kawo walwala a yankin na Gaza.

Amurka da Isra'ila sun nuna damuwa a kan cewa makamai, ko masu hada makaman, za su iya ketarawa zuwa Gaza; amma kasar ta Masar ta jajirce cewa za ta yi bincike mai tsanani a kan duk wanda zai ketara iyakar.

Bude iyakar dai alama ce da ke nuna cewa sababbin mahukuntan Masar ba za su baiwa Isra'ila hadin kai ba, kamar yadda tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak, ya yi.