Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Wankan jego

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Wakan jariri na gargajiya

Shirin wannan makon zai duba batun wankan jego da kuma irin kulawar da yakamata mai jego ta samu da jaririnta.

Mu je birnin Maiduguri a Najeriya don jin yadda lafiyar malama Fatima bakuwar Haifi ki yaye da BBC Hausa da ta haihu 'yan watannin baya da jaririyarta Rukayya suke.

To sai dai kuma yayinda masana al'adun hausawa na gargajiya ke fadi tashi da hasashen ko daga ina bahaushe ya aro al'adar wankan jego, idan har arowar yayi, zaku ji abinda wasu Malaman addinin musulunci ke cewa.

Zaku kuma ji daga masana a fannin kiwon lafiya domin jin yadda batun wankan jego yake a gurinsu.

Ayi sauraro lafiya.