Ratko Mladic zai iya fuskantar shari'a

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Za'a tasa keyar Ratko Mladic zuwa kotun hukunta manya laifuka a Hague.

Wani alkali a Serbia ya yanke hukuncin amika tsohon kwamandan sojojin Serbia Ratko Mladic, zuwa kotun hukunta laifukan yaki ta duniya a Hague domin ya fuskanci shari'a.

Amma lauyansa ya ce za su daukaka kara kan hukuncin.

Tunda farko lauyan na sa (Milos Saljic), ya ce Janar Mladic, ba shi da koshin lafiyar da zai fuskanci shari'ar kisan kare dangin da ake zarginsa da aikatawa.

Maya Ko-vach-ye-vich shi ne mai magana da yawun Likitocin; "Mun tabbatar cewa Ratko Mladic, yana da koshin lafiyar da za a iya mikashi zuwa Hague, saboda mun gudanar da dukkan gwaje-gwajen da suka kamata.

'Yan sanda sun kama tsohon kwamandan dakarun Sabiyawan Bosniya, Ratko Mladic a Sabiyawa, shekaru goma sha shidda, bayan an zarge shi da aikata laifukan yaki, a lokacin rikicin Bosniya.

Kame Mladic

Shugaban kasar Sabiya, Boris Tadic ne ya bada sanarwar kamun nasa.

Ya ce, "a madadin jamhuriyar Sabiya, ina bada sanar da cewa a yau mun cafke Ratko Mladic.

Muna kuma shirin mika shi ga kotun musamman dake Hague."

Sa'o'i bayan bada sanarwar kamun nasa, jama'a ta taru a wani dandali na tsakiyar Belgrade, babban birnin kasar, suna kada tutoci, suna kuma kiran da a sako Janar Mladic.

Ya kasance yana ci gaba da walwala a Belgrade, har zuwa 2002.

Tuni dai Ratko Mladic ya bayyana a gaban wata kotu ta musamman a birnin Belgrade, inda wani alkali mai bincike zai yanke shawarar ko ya dace a mika shi ga kotun duniya mai shari'ar laifukan yaki a birnin Hague.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar adadin mutanen da suka mutu a Bosnia

Kalubale

Jami'ai sun ce bisa dukkan alamu mutumin mai shekaru sittin da tara zai kalubalanci kokarin ingiza keyarsa, kuma za a iya kwashe kwanaki bakwai ana jayayya kan batun.

Slobodon Homen jami'i ne na ma'aikatar shari'a:

Ya ce "Mladic na nan a wannan kasa, kuma Sabiya na mutunta kaidojin shari'a."

Babban laifin da ake zarginsa da aikatawa shi ne kisan kare dangi na Srebrenica a Bosnia, cikin 1995.

Musulmi maza da yara kanana kimanin dubu takwas ne dakarun Sabiya suka kashe, bisa umurnin Janar Mladic.

Ana dai ta samun sakonnin marhabin da kamun Janar Mladic daga sassa daban daban.

Shugaba Obama ya jinjina wa shugaban Sabiya , Boris Tadic kan jajircewar da yayi, har sai da ya gano shi, ya kuma yi fatan cewa dangin wadanda Janar Mladic din ya sa aka halaka, zasu dan samu kwancyar hankali , sakamakon kamun nasa.

Shugaban faransa Nicolas sarkozy shi ma ya yaba da namijin kokarin da Shugaba Tadic ya yi.

Ministan harkokin wajen Sweden Cal Bildt, wanda tsohon jakadan tarayyar turai ne a yankin Balkans, ya ce hukumomin Sabiya sun bada kariya , na wani dan lokaci ga Janar Mladic, amma kwazon jami'an ayyukan sirri na shugaba Tadic, a karshe suka tabbatar da kamun nasa.