Yara dubu 35 sun tsere daga gidajensu a Abyei

Garin Abyei kafin a tarwatse
Image caption Garin Abyei kafin a tarwatse

Kungiyar agaji ta Save The Children ta ce fada a yankin Abyei na kasar Sudan, wanda ake takaddama a kansa, ya tilastawa yara dubu talatin da biyar barin gidajensu.

Yankin ne dai tushen tayar da jijiyoyin wuya tsakanin arewacin kasar, wanda dakarunsa suka mamaye yankin, da kuma kudancin kasar, mai shirin karbar 'yancin kai a watan Yuli.

Tashe-tashen hankula sun karu a yankin na Abyei ne tun bayan da fada ya barke a farkon wannan watan.

Kungiyar agajin ta Save The Children ta ce kusan daukacin al'ummar yankin sun gudu daga gidajensu yayin da ake samun rahotannin harbe-harbe da kone-kone da kuma kwasar ganima.

Kungiyar ta ce an kuma raba da yawa daga cikin yara dubu talatin da biyar din da danginsu.

Kungiyar ta Save The Children ta ce a shirye ta ke ta tunkari wannan kalubale, amma fadan da ake ci gaba da fafatawa yana hana kayan agaji kaiwa wuraren da abin ya fi shafa.