Anci tarar tsohon shugaban kasar Masar

Wata kotu a Masar ta ci tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak, tarar dala miliyan tasa'in, tare da wasu tsoffin manyan jami'an gwamnatinsa biyu.

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta same su da laifin katse hanyoyin sadarwa na salula da internet, a lokacin zanga zangar nunawa gwamnatin tasu kyama, a watan Janairu.

Wannan ne hukuncin farko da aka yankewa mista Mubarak, tun bayan da aka kawar da shi daga mulki.

Yanzu haka mista Mubarak na fuskantar wasu manyan tuhumce-tuhumcen da suka hada da bada umurnin a kashe masu zanga zanga. Idan an same shi da laifi za'a iya yanke masa hukuncin kisa.

Sauran jami'an biyu da aka ci tarar sune: tsohon Praministan kasar, Ahmed Nazif, da kuma tsohon ministan cikin gida, Habib al Adly.