Za'a kece reni a fagen taka leda

Nan gaba a yau ake shirin yin karon battar-karfe, tsakanin biyu daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya - wato Barcelona da Manchester United - a zagayen karshe na gasar cin kofin kwallon kafa ta Champions League.

Za ai karawar ce a filin wasan Wembley da ke nan London.

Barcelona da Manchester dai kowanensu zai yi kokari ne ya lashe kofin a karo na hudu.

Ana hasashen cewa, mutanen da za su kalli wasan kwallon ta gidan talabijin a ko'ina a duniya, za su kai miliyan dari ukku.

Barcelona da Manchester United sun taba karawa sau daya, a zagayen karshe, shekaru biyu da suka wuce, inda Barcelona ta yi nasara da ci biyu da nema.