An makaro a kasafin kudin bana a Najeriya

A Najeriya, wasu masana tattalin arziki na ganin cewa, rashin sanya hannu a kan kasafin kudin wannan shekara da wuri, zai shafi habakar tattalin arzikin kasar.

A jiya ne dai Shugaba Goodluck Jonathan ya sawa kasafin kudin hannu, kwana biyu kamin a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.

Kasafin kudin na bana ya kai kimanin naira Triliyan hudu - ko kuma dala biliyan ashirin da tara.