Jamus ta zargi Spaniya da baza cutar E-coli

Hakkin mallakar hoto AFP

An ci gaba da takaddama game da barkewar kwayar cutar E- Coli da ta barke a wasu kasashen nahiyar Turai.

Akalla mutane goma sha hudu ne suka rasu a Jamus, ana kuma zaton daruruwa a Sweden da Denmark da Netherlands da kuma Birtaniyasun kamu da cutar.

Ana kuma ci gaba da faman kace- na- ce game da tushen cutar.

Jami'an Jamus sun dora alhakin ne akan wani gurji da ake shigowa dashi daga Kasar Spaniya, sai dai Ministan lafiya na kasar ya ce babu shaidar hakan gaske ne, kuma Spaniya za ta nemi diyya akan wadanda ke zargin gonakin ta.