'Yan gudun hijira sun tsero Nijar daga Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A jamhuriyar Nijar wasu alkaluma da Hukumomin Kasar suka fitar sun tabbatar da cewa fiye da 'yan gudun hijira dubu casa'in da tara ne daga kasashen Libya da Ivory Coast suka isa Kasar sakamakon barkewar yake -yake a wadannan kasashen.

Mafi yawancin wadanda suka gudu din sun yi kaura ne daga kasar Libya, inda suka isa garin Agadez mai makwabtaka da Libya ta hanyar amfani da motoci, cikin yashin Sahara.

Da dama daga cikin su sun ce sun fuskanci matsaloli daban- daban kamar barazana ga rayuwarsu, da yunwa, da kishirwa ko kuma asarar dukiya yayin da suke barin Kasar ta Libya.

Sai dai wani kalubalen da 'yan gudun hijirar ke ci gaba da fuskanta shi ne na rashin muhalli ko jarin da za su rike kansu bayanda suka isa Nijar.