Dakarun soji sun nemi gafara kan harin Afghanistan

Wani dakaren soja a Afghanistan Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dakarun soji sun nemi afuwa a Afghanistan

Dakarun kasashen waje da ke Afghanistan sun nemi afuwa game da harin da suka kai a kudancin kasar a jiya Lahadi, abin da ya halaka mutane goma sha hudu.

A cikin wani jawabi da babban janar din NATO ya yi, ya ce babban abin da suka fi mayar da hankali akai shi ne kare fararen hula daga hare-hare, don haka suna neman afuwa bisa kuskuren da suka yi.

Da farko shugaban Afghanistan Hamid Kharzai, ya yi Allah-wadai da wannan hari, inda ya ce gwamnatinsa ta sha gargadin Amurka da kada ta kuskura ta kai irin wannan hari ta sama.

Sai dai fadar White House ta ce ta nuna damuwarta game da hare-haren.