Za mu gudanar da zabe, in ji FIFA

Shugaban fifa, Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fifa za ta gudanar da zabe

Hukumar da ke kula da kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce za ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben shugabancin hukumar, wanda za a yi a wannan makon.

Gudanar da zaben zai kasance wata al'ada ce kawai tun da dai dan takara daya tilo a zaben shi ne Sepp Blatter, wato shugaban hukumar mai ci .

Tuni dai hukumar FIFA ta dakatar da sauran abokan hamayyar Mista Blatter, wato Mohammad Bn Hammam da Jack Warner inda ta ce tana bincike akansu.

Hamman da Warner sun zargi Blatter da aikata cinhanci, sai dai kwamatin da Fifar ta nada don gudanar da bincike kan batun ya wanke shi daga zargin.

Don haka babban sakatare janar na hukumar Jerome Valcke, ya ce za a gudanar da zaben tun da dai ba a sami Blatter da laifi ba.