Akalla masu zanga zanga 20 ne aka kashe a Yemen

Hakkin mallakar hoto REUTER
Image caption Masu zanga zanga a Yemen

Jami'an kiwon lafiya a kasar Yemen sun ce mutane akalla 20 ne aka kashe a birnin Ta'iz, lokacin da dakarun dake biyayya ga shugaba Ali Abdullah Saleh, suka bude wuta a wani sansani na masu zanga zangar nuna kyamar gwamnati.

Wani likita a birnin ya shiadawa BBC cewa akwai mutane sama da dari da suka jikkata, lokacin da sojoji suka kutsa kai cikin masu zanga zangar, suna harbe harbe suna kuma kona tantuna.

Daga bisani manya motocin sharar hanya sun kawar da duk wani abin dake cikin sansanin.

Wasu mazauna birnin Zinjibar na gabar teku sun ce mayakan sama na kasar ta Yemen sun rika kai hare haren bam a kan wasu wurare da 'yan bindigar da suka kwace iko da garin kwanakin baya , suke.