Jacob Zuma ya kai ziyara Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jacob zuma tare da Kanal Gaddafi

Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya bar birnin Turabulus na kasar Libya, inda ya tattauna da Kanar Gaddafi, a kokarin warware rikicin kasar Libyar ta hanyar diplomasiyya.

Shugaban Libyar na fuskantar matsin lamba, sakamakon hare hare ta sama da jiragen saman yakin kungiyar NATO ke kai masa.

Rasha, daya daga cikin muhimman kasashen dake mara masa baya, ta janye goyon bayan da take masa.

Daya daga cikin mashawartan Kanar Gaddafi ya shaidawa BBC cewa babu alamun cewa zai sauka daga karagar mulki.

Babu karin bayani, kan sakamakon ziyarar.

Wata makamanciyar ziyarar da Mr Zuma ya kai cikin watan jiya, a wata tawagar wakilan kungiyar tarayyar Afrika, ba ta haifar da wani sakamako na a-zo-a-gani ba.