Boko Haram ta dauki alhakin kai hari a Bauchi da Zuba da Zaria

Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Borno Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Borno

Kungiyar nan ta Jama'atu Ahl- Sunnati Lil da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, ta ce ita ce ke da alhakin dana bama-baman da aka yi a garuruwan Bauchi da Zaria da Zuba a cikin karshen mako.

Haka nan kuma kungiyar ta ce ita ce ke da alhakin hallaka kanen Shehu Borno, Alhaji Abba Anas Ibn Umar Garbai El Kanemi.

Mataimakin Kakakin Kungiyar wanda ya ce sunansa Abu Zaid ne, ya shaidawa BBC haka.

Bama-Baman dai sun yi sanadiyar hallaka mutane akalla goma sha shidda, yayin da wasu da dama suka samu raunika.