An harbe dan uwan Shehun Borno

Jana'izar kanin Shehun Borno
Image caption Jama'a na halartar jana'izar kanin Shehun Borno

Wasu 'yan bindiga sun harbe kanin Shehun Borno, Alhaji Abba Anas Ibn Umar Garbai El Kanemi jiya da daddare a kofar gidan sa, dake unguwar Kangamari dake yankin karamar hukumar birnin Maiduguri da kewaye.

Rundunar Yansandan jihar Borno ta tabbatar da abkuwar lamarin da cewar wannan na daga cikin irin kashe kashen da yan kungiyar nan ta Boko Haram suka saba kaddamarwa kimanin sama da watanni goma a birnin na Maiduguri da ma wasu sassan jihar.

Marigayin dai kane ne ga Mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar Garbai Al Amin El Kanemi kuma a dazu dazun nan ne aka yi jana'izar sa a fadar shehun.

Ana ta dai fama da hare-hare a garin na Maiduguri da wasu sassan Arewacin Najeriya a 'yan kwanakin nan. Sai dai mahukunta na cewa suna iya kokarinsu domin shawo kan matsalar.