Cikas wajen zaben sabon shugaban FIFA

Kungiyar Kwallo kafa ta duniya, FIFA Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Kungiyar Kwallo kafa ta duniya, FIFA

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA ta bukaci hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA da ta dage gudanar da zaben da za a gudanar gobe Laraba, inda shugaba mai ci, Sepp Blatter ke tsayawa takarar shugabancin hukumar, ba tare da hamayya ba.

Hukumar ta ce dimbin zargin da ake da shi kan cin hanci da rashawa, ya sa yana da muhimmanci a ce an samu wani da zai fafata da shi wajen neman mukamin.

Wakilin BBC ya ce, hukumar kwallon kafar ta Ingila, da tafi kowace tsufa a duniya, kusan sai a kurarren lokaci ta yunkuro, domin samun goyon baya a matakin nata.

Ta yi kiran ne yayinda wakilai ke hallara a Zurich dominhalartarv taron shekara shekara na hukumar ta FIFA.