Mladic ya isa kotun laifuka ta duniya

Hakkin mallakar hoto AP

Kasa da mako guda bayan cafke tsohon kwamandan dakarun Sabiyawan Bosniya, Ratko Mladic, a yanzu ya isa kasar Holland, inda kotun shari'ar laifukkan yaki ta duniya dake Hague, ke zarginsa da aikata kisan kare dangi.

Ministan shari'a na Sabiya ne ne ya rattaba hannu a kan umurnin tasa keyar Mr Mladic din, bayan kotu ta ki amincewa da karar da ya daukaka, yana kafa hujja da rashin koshin lafiya.

Snezana Malovic ita ce ministar shari'ar Sabiya, ta ce sakamakon mika Ratko Mladic ga kotun duniya a Hague, jamhuriyar Sabiya ta sauke nauyin dake kanta, da kuma alkawarin da ta yi ma duniya.

Mr Mladic zai shiga cikin jerin mutane sama da talatin da ake tsare da su bisa zargin aikata laifukkan yaki a tsohuwar Yugoslavia.