Korar farar hula daga barikokin sojan Najeriya

Sojan Najeriya
Image caption Sojan Najeriya

Wasu 'yan Nijar da ke gudanar da harkokin kasuwanci a barikin sojan Calabar, a jahar Cross River, sun yi kukan cewa hukumomin sojan sun kore su daga can.

Farar hula da dama ne dai ke zaune a barikokin sojan Najeriya, inda suke gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwannin da ake kira Mammy Market.

Sai dai a baya bayan nan an yi fama da tashe tashen bam a irin wadannan kasuwannin, inda aka sami hasarar rayuka.

Hukumomin sojan dai sun ce ba 'yan Nijar ne kawai su ka kora ba, kuma sun dauki matakin ne domin kara tabbatar da tsaro a barikokin nasu.