Tunawa da matan da mazajensu suka rasu

Matan da mazajensu suka rasu a Iraki Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Matan da mazajensu suka rasu a Iraki

Yau Alhamis din nan ce, 23 ga watan Yuni, a karon farko, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe, domin tunawa da matan da mazajensu suka mutu.

Ana yin hakan ne domin fito da irin halin kaka-ni-kayin da irin wadannan mata ke shiga, da kuma irin wariyar da suke fuskanta, bayan rashin mazajen nasu. Cikin watan Disamban bara ne, babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kada kuri'ar amincewa da ranar, bayan wani kudiri da kasar Gabon ta gabatar.

Wani dan siyasar Birtaniya ne ya fara jagorantar wannan yunkuri, ganin cewa ya tashi maraya wajen mahaifiyarsa, bayan rasuwar mahaifinsa a Indiya.

An kiyasta cewa daga cikin irin wadannan mata miliyan 245 a duniya, miliyan 115 na fuskantar rashin adalci, da talauci da kuma azabtarwa.