Murnar tafiyar shugaba Saleh Saudiyya

Shagulgula a Yemen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shagulgula a Yemen

A Yemen dubban jama'a suna ta shagulgula bayan da shugaban kasar Ali Abdullah Saleh ya tafi Saudiyya neman magani, sakamakon harin da aka kaiwa fadarsa a ranar Juma'a. Tuni da ma wasu manyan ministocinsa suka riga shi zuwa Saudiyyar, bayan sun sami munanan raunuka a harin na Juma'a.

Akwai jita-jitar cewa shugaba Saleh ba zai sake komawa kasar ta Yemen ba.

A yau ma an sami hasarar rayuka a wasu hare-haren da aka kai a kasar.

Tuni Jakadan Amirka a Yemen din ya gana da mukaddashin shugaban kasar, Abd-Rabbu Mansur Hadi - wanda a yanzu shi ne shugaban kasar na riko - domin tattauna halin da ake ciki.

Akwai yiwuwar shugaba Ali Abdallah Saleh zai zama shugaba na ukku - bayan Ben Ali na Tunisia da Hosni Mubarak na Masar - wanda guguwar sauyin da ta kada a kasashen Larabawa, za ta yi awon gaba da shi.