An yi jana'izar wani dan jarida a Pakistan

An yi jana'izar wani dan jarida a Pakistan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin jami'an tsaron Pakistan da hannu a kisan Saleem Shahzad

Daruruwan mutane ne a garin Karachi na kudancin Pakistan suka halarci jana'izar wani dan jarida mai binciken kwakwaf, Saleem Shahzad, da aka yi wa kisan gilla.

Ajiya ne aka tsinci gawar Mr Shahzad, kuma akwai tabban dake nuna cewa an yi matukar gana masa azaba.

Wakiliyar BBC ta ce Pakistan na daga cikin kasashe mafiya hadari ga 'yan jarida. Ana kwatanta ta da kasashe irinsu Afgahnistan da Somalia.

A kwanakin baya ne Mr Shahzad ya yi wata kasida inda yake nuna akwai alaka tsakanin kungiyar al-Qaeda da rundunar mayakn ruwa ta Pakistan.

Wakilin Kungiyar kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch a Pakistan ya zargi hukumar leken asirin da hannu wajen sace Mr Shahzad--zargin da su kuma suka musanta karara.