An nemi a mika shugaban Syria kotun duniya

Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zangar adawa da gwamnati da dama ne aka kashe a Syria

Kasar Australia ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta duba yiwuwar mika shugaban kasar Syria Bashar al-Assad, zuwa kotun duniya mai hukunta laifukan yaki.

Australia ta koka ne kan yadda shugaba al-Assad ya fuskanci masu zanga-zangar adawa da mulkinsa.

Ministan harkokin wajen kasar Kevin Rudd, ya bada misali ga cin zarafin wani saurayi dan shekaru 13 Hamza al-Khatib.

Mutuwar saurayin da kuma hoton bidiyon mai tada hankali na makomarsa, na daya daga cikin dalilan da suka sanya Kevin Rudd ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da ya gurfanar da Mr al-Assad a gaban kotun ta Hague.

Mr Rudd ya ce, irin abubuwan da gwmanatin Syria ke aikatawa akan al'ummarta da kuma azabtarwa tare da kashe wannan yaron, ya sanya babbar alamar tambaya game da sahihancin hukumomin kasar ta Syria.

Amurka ma ta koka

Haka kuma dangane da batun kisan yaron, Amurka ita ma ta fara nuna damuwarta game da abin dake faruwa a Syria.

Sakatariyar kula da harkokin wajen Amurka Hilary Clinton, ta fito fili ta bayyana kokwantonta game karfin ikon Mr Assad, alamar dake nuna yiwuwar duba makomar Syria ba tare da shugaban Assad a matsayin shugabanta ba.

A daukacin makonni goman da aka shafe ana rikici a kasar ta Syria, matsin lambar kasashen ketare na zuwa ne kan mukarraban shugaba Assad, amma ba shi kansa ba.

Manufar dai ita ce, a ba shi mafita, ta yadda zai jagorancin sauyi a kasar.

Idan dai har gwamnatin Syria ta fadi, zai yi babban tasiri a yankin musamman ma ga kasar Lebanon.