Gwamnatin Bauchi zata biya diyya ga.....

Yanzu haka ana tayar da jijiyoyin wuya a jihar Bauchin Nijeriya sakamakon wani mataki da gwamnatin jihar ta dauka na tallafawa wa iyalan masu yi wa kasa hidima su goma, wadanda suka rasa rayukansu a jihar, a tashin hankalin bayan zabe da aka yi a watan Afirilu. Gwamnatin jihar Bauchin dai ta bayyana cewa zata biya iyalan matasa masu yi wa kasa hidimar kudi naira muliyan bibbiyu, kana ta ilmantar da uku daga cikin 'yan-uwan kowane dayansu tun daga Firamare har zuwa jami'a kyauta, sannan kuma zata bai wa iyayensu kujerun aikin Hajji a Saudiyya ko kuma ziyarar ibada ta kirista a Isra'ila, gwargwadon addinin da suke bi. To sai dai kuma 'yan adawa a jihar na ganin cewa suke yi matakin rashin adalci ga sauran wadanda suka rasa rayukansu a tashin hankalin wanda suka dora akan matakin magudi na jam'iyyar PDP.