Yau za a gudanar da zaben shugaban FIFA

Shugaban FIFA, Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yau za a gudanar da zaben shugaban FIFA

Shugaban hukumar kallon kafa ta duniya, FIFA, Sepp Blatter na kan hanyarsa ta sake darewa shugabancin hukumar a karo na hudu.

Batun zargin cin hanci a hukumar kwallon kafan dai, ya kankane hukumar gabanin zaben shugaban da za a gudanar a yau Laraba.

Zargin cinhancin ya sanya Fifa ta dakatar da manyan jami'anta guda biyu, wato Muhammad Bn Hammam da Jack Warner daga cikinta.

A jiya ma sai da hukumar kwallon kafa ta Ingila, da takwararta ta yankin Scotland suka bukaci a dakatar da zaben, saboda zarge-zargen cinhanci a Fifar.