Rahoto kan tashar nukiliyar Japan

Jami'an hukumar kula da nukiliya ta duniya lokacin da suka je Japan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Japan ta raina matsalar girman matsalar nukiliya'

Hukumar da ke kula da makamashin nukiliya ta duniya ta ce Japan ta raina girman matsalar da tsunami ta janyo a tashoshin nukiliyarta.

A wani rahoto da ta fitar game da tashar nukiliya ta Fukushima, hukumar ta jaddada muhimmancin samar da masu kula da sha'anin nukiliya masu zaman kansu a kasar.

Rahoton ya ce kusan watanni uku kenan bayan hatsarin da ya aukawa tashar nukiliyar ta Japan, amma har yanzu turiri na fita daga cikinta. Za a tattauna kan wannan rahoto a wani taro kan inganta tsaro a tashoshin nukiliya,wanda za a gudanar a Vienna nan gaba a cikin wannan watan.