Shawarwari kan nadin ministoci a Najeriya

Dakta Goodluck Jonathan
Image caption Shawarwari kan nadin ministoci a Najeriya

A Najeriya,'yan kasar sun baiwa shugaba Goodluck Jonathan shawarwari kan irin mutanen da ya kamata ya nada a matsayin ministoci a gwamnatinsa.

A cewar masu lura da al`amura siyasan, shugaban kasar na da babban kalubale a gabansa na fitar da mutanen da zai baiwa mukamai, inda suka ce ya kamata ya yi la`akari da cancanta maimakon ba da fifiko ga siyasa.

Malam Abubakar Kari na jami'ar Abuja, ya shaidawa BBC cewa, ya kamata shugaban ya gujewa bara-gurbin mutane a lokacin da zai nada jami'an gwamnatinsa.

Ya ce hakan ne kawai zai magance matsalolin da kasar ke fama da su.